BREAKING NEWS

Labaran Safiyar Asabar 19/02/2022CE - 17/07/1443AH. Cikakkun labaran

Gwamnan Borno, Babagana Zulum ya bai wa tubabbun 'yan daba su 152 tallafin kudi Naira miliyan 100 su ja jari bayan koyar da su sana'a.

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da ɗan basarake da wasu 7 a jihar Taraba, sun nemi a tattara musu miliyan 70.

Majalisar zartaswa ta Tarayya ta amince da kashe Naira bilyan 1.2 na aikin titin jirgin ƙasa Dala Lagos zuwa Ibadan da kuma Fatakwal zuwa Maiduguri.

Wasu ƙungiyoyi sun bai wa Shugaba Buhari wa'adin nan da ranar 22 ga wannan watan ya sanya hannu a sabuwar dokar zaɓe ko su yi zanga-zanga.

Wata kotu a Abuja ta yanke wa wasu tsofaffin 'yan sanda 2 hukuncin kisa bisa samunsu da laifin fashi da makami.

Hukumar EFCC ta mika wa Hukumar NHIS Naira bilyan 1 da wasu bankunan kasuwanci suka rike.

Mutane 17 sun mutu a hadarin motar dakon mai da ta kama da wuta a jihar Ogun.

Jakadan Rwanda a China na sayar da gahawa ta TikTok.

Ƙasar Mali ta umarci sojojin Faransa su gaggauta ficewa daga cikinta.

Wata kotu a India ta zartas da hukuncin kisa kan mutane 38 saboda harin 2008.

Harry Maguire ya musanta jita-jitar rikici tsakaninsa da Cristiano Ronaldo dangane da mukamin Kaftin.

Comments

Popular posts from this blog

News

THE HISTORY OF PROPHET ADAM AS